in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hana 'yan wasan kasar Rasha su halarci gasar wasannin Olympics ta nakasassu laifi ne
2016-08-31 13:52:15 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova, ta bayyana a kwanakin baya cewa, hana 'yan wasan kasar su halarci gasar wasannin Olympics ta nakasassu laifi ne da aka aikata.

Zakharova ta bayyana yayin da take zantawa da wakilin gidan rediyo na Izvestia a kwanakin baya cewa, an nunawa 'yan wasan nakasassu na kasar Rasha banbanci, kuma hana dukkan 'yan wasan nakasassu na kasar Rasha su halarci gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Rio laifi da bai dace a aikata shi ba.

Sannu a hankali dai kasashen duniya za su game kuskuren da wannan kotu ta yanke, duba da cewa ta yi hukuncin ne bisa matsin lamba da aka yi mata.

Kafin wannan, firaministan kasar Rasha Medvedev ya bayyana cewa, hana 'yan wasan kasar Rasha su halarci gasar wasannin Olympics ta nakasassu kuduri ne na rashin adalci. Medvedev ya bayyana cewa, kudurin da aka tsaida na hana 'yan wasan nakasassu na kasar Rasha su halarci gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Rio, rashin kunya ne, wanda ya cutar da nakasassu, zai kuma hana su nuna kwazon su.

Medvedev ya bayyana cewa, ana bukatar ci gaba da yaki da shan maganin kara kuzari yayin da ake gudanar wasanni. Kaza lika ya dace a yi tir da amfani da maganin kara kuzari, da yanke hukunci ga wadanda suka aikata hakan, amma ana bukatar samun cikakkun shaidu ta hanya mafi dacewa kuma bisa doka.

A ganinsa, kashi 80 cikin dari na binciken batun yaki da maganin kara kuzari a kasar Rasha, basu ne na siyasa kadai, yayin da kuma kashi 20 cikin dari kacal ne ke da nasaba da hakikanin batun shan maganin kara kuzarin. Ya ce wasu hukumomin wasanni na duniya suna karkashin jagorancin kasar Amurka ne, kuma kotun yanke hukunci game da sha'anin wasanni ta duniya ta tsaida irin wannan kuduri ne, don kawar da wannan babbar 'yar hamayyar kasar Amurka wato kasar Rasha.

A ranar 23 ga watan Agusta, kotun yanke hukunci game da wasanni ta duniya, ta sanar da watsi da rokon da kwamitin wasannin Olympics na kasar Rasha yayi game da hana 'yan wasa nakasassu na kasar sa halartar gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Rio. Kuma ga alama 'yan wasa nakasassu na kasar ta Rasha ba za ta halarci gasar a wannan karo ba. Matakin da Rashan ta yi Allah wadai da shi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China