Kwamitin sulhun MDD ya shirya muhawara mai taken "kananan yara da rikice-rikice", inda aka nazarci rahoton shekara-shekara da babban sakataren MDD ya gabatar game da wannan batu.
A jawabinsa yayin muhawarar, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, a lokacin da aka samu barkewar rikice-rikice an kashe ko an ci zarafin karanan yara wanda har ya kai su ga nakasa, kana an lalata gidaje da makarantunsu. Kananan yara suna fuskantar mawuyacin hali a kasashen Iraki, Nijeriya, Sudan ta Kudu, Somaliya, Syria, Yemen da sauransu. Ban da wannan kuma, masu tsattsauran ra'ayi sun kawo babbar illa ga tsaron kananan yara.
Hakazalika kuma, Ban Ki-moon ya yi kira ga bangarori daban daban da rikice-rikice suke shafa da su tabbatar da tsaron makarantu da asibitoci da fararen hula, sannan kuma kada su sanya kananan yara a cikin aikin soja. Kana ya kalubalanci bangarori daban daban da su gaggauta daukar matakai don magance dalilan da ke haddasa fararen hula suke barin muhallansu. (Zainab)