A ranar Laraba da safe, Koriya ta Arewa ta harba makaman roka guda biyu zuwa gabashi inda kuma daya daga cikinsu ake zaton ya fada yankin teku na tattalin arziki na kasar Japan.
Mista Dujarric ya bayyana cewa, wadannan ayyuka na Koriya ta Arewa na kasancewa wani tarnakaki ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar, kana ba zai tamakawa kwantar da tashe-tashen hankali a wannan yankin Koriyar ba.
Muna sake jaddada kira ga Koriya ta Arewa da ta yi la'akari da bukatar gamayyar kasa da kasa ta kawar da manufofinta tare da dawowa cikin shirin tattaunawa na gaskiya, in ji mista Dujarric a yayin wani taron manema labarai.
Kwamitin sulhu ya yi wani kebabban taro a ranar Laraba domin tattaunawa game da gwaje-gwajen makaman RPDC.
Harbin ya gudana makwanni biyu bayan gwaje-gwaje guda uku na makaman roka masu cin gajeren zango, lamarin kuma ga dukkan alamu domin yin alla wadai kan matakin hukumomin Seoul da Washington na kafa tsarin kakkabo makaman roka sunfurin THAAD a Koriya ta Kudu. (Maman Ada)