in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin raya al'adu
2015-09-17 10:22:16 cri

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar Sin ya sanar da kulla yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin sa da hukumar kididdigar kasa da kasa ta Amurka wato IDG da kungiyar yada ilimin labarin kasa ta Amurka NGS a Washington, kuma ana sa ran bangarorin uku za su karfafa mu'amala da hadin gwiwa a fannin musayar al'adu tsakanin kasashen biyu.

Mataimakin daraktan ofishin kula da yada labarai na majalisar gudanarwar Sin Guo Weimin, da mataimakin shugaban kungiyar yada ilimin labarin kasa ta Amurka Terry Adamson, sai kuma mataimakin hukumar IDG Xiong Xiaoge dukkannin su sun halarci bikin rattaba hannu.

Mr. Guo ya ce, yanzu Sinawa sun kara fita zuwa kasar Amurka da sauran kasashen duniya don yawon bude ido ko kasuwanci, kuma karin 'yan kasashen waje ciki har da Amurkawa sun ziyarci kasar Sin. A karkashin wannan shiri, na hadin gwiwa tsakanin bangarorin uku, zai yi matukar amfani wajen samar da fahimtar juna tsakanin jama'ar kasashen Sin da Amurka, kuma ya kasance wani muhimmin ci gaba ta fuskar musayar al'adu tsakanin kasashen Sin da Amurka a gabannin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a Amurka.

A bisa takardar yarjejeniyar da aka kulla tsakanin bangarorin biyu, hukumar IDG za ta taimakawa kungiyar yada ilimin da ya shafi labarin kasa ta Amurka don yin amfani da hotunan da take da su, wajen shirya bikin nune-nunen hotuna tsakanin kasashen biyu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China