in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna kin amincewa da maganar Shinzo Abe
2016-08-29 13:59:46 cri
Firaministan kasar Japan Shinzo Abe, ya bayyana a bikin bude taron shugabannin Japan da Afirka wanda aka shirya a birnin Nairobi na kasar Kenya a kwanakin baya cewa, tekun Indiya da na Pasifik sun hade nahiyar Asiya da Afirka, don haka kasar Japan na da nauyin raya yankunan tekun don zama yankuna da za a gudanar zirga-zirga cikin 'yancin da girmama dokoki.

Dangane da maganar da Shinzo Abe ya yi, Zhang Ming, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, wanda ya halarci bikin rufe taron shugabannin Japan da Afirka a jiya Lahadi 28 ga wata bisa gayyatar da aka yi masa, ya furta a gaban manema labaru cewa, adadin kudin cinikayya tsakanin bangarorin Sin da Afirka a shekarar 2015 ya kai dalar Amurka biliyan 180, inda da dama daga cikin kayayyakin da ake cinikayya tsakanin bangarorin 2 an yi jigilar su ne ta hanyar teku, kuma ana bi ne ta tekun Indiya da Pasifik. Ban da ciniki da kasashen Afirka, kasar Sin ta yi amfani da layin don gudanar da harkokin cinikayya da yankin gabas ta tsakiya gami da Turai. A saboda haka, tun ba yau ba akwai 'yancin zirga-zirga sosai a wadannan yankunan teku .

A cewar jami'in kasar Sin, a yayin taron da aka kira a wannan karo, dukkan shugabannin kasashen Afirka da suka yi jawabai sun ki mayar da taron a matsayin maganar siyasa, lamarin da ya sanya kasar Japan kin cewa komai, wannan ya sa a karshe ta soke wasu abubuwa daga cikin takardar da take son gabatar da ita a karshen taron. Hakan, a cewar Zhang Ming, ya shaida karfin adalci.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China