A cewar jami'in na kasar Sin, ya kamata a mai da hankali kan sakamakon da aka cimma, da kuma matakan da aka dauka a maimakon alkawarin da aka yi, yayin da ake tantance huldar hadin gwiwa tsakanin wasu kasashe da kasashen Afirka. Sai dai a nata bangare, kasar Sin bisa matsayinta na wata kasa mai muhimmanci wanda ke jagorantar aikin hadin kai tare da kasashen Afirka, tana fatan ganin karin bangarori masu huldar hadin gwiwa tare da nahiyar Afirka. Ban da haka kuma, kasar Sin na son yin kokari tare da sauran bangarorin duniya wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Afirka, don neman samun ci gaba tare, gami da samun moriya ta bai daya.(Bello Wang)