A yayin ganawar, shugaba Xi ya bayyana matsaya da kuma muhimman sakamako da aka cimma a yayin taron kolin, wato bangarori daban daban da suka halarci taron sun kuduri aniyyar bullo da hanyar da za a bi wajen bunkasa tattalin arzikin duniya, da kirkiro sabbin hanyoyin neman ci gaba, don kara ingiza karfin tattalin arzikin duniya, kana da kyautata tsarin sarrafa tattalin arziki da hada-hadar kudi na duniya don daga karfin tinkarar kalubalen tattalin arziki a duniya, da farfado da muhimmiyar rawar da harkokin cinikin kasa da kasa da zuba jari suke takawa don bullo da tsarin tattalin arziki mai bude kofa na duniya, da kuma sa kaimi ga samun ci gaba ta hanyar yin hadin gwiwa, ta yadda duniya za ta amfana ta hanyar hadin gwiwar dake tsakanin membobin kungiyar G20.(Bilkisu)