in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi jawabi a yayin bikin rufe taron G20
2016-09-05 19:51:26 cri

A yau Litinin da misalin karfe 5 da yamma agogon kasar Sin ne, aka rufe taron kolin G20 da aka gudanar a birnin Hangzhou da ke nan kasar Sin. A jawabin ya gabatar a yayin rufe taron shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya nuna cewa, a bisa kokarin da aka yi, shugabannin kungiyar G20 da suka halarci taron sun cimma muhimmin ra'ayi bai daya kan wasu batutuwa bayan tattaunawar da suka yi.

Xi ya ce, da farko shugabannin sun yi kuduri aniyar bullo da hanyar da za a bi wajen bunkasa tattalin arzikin duniya. A yayin da tattalin arzikin duniya yake fuskantar hadari da kalubale, ya kamata a ci gaba da yin cudanya da daidaito kan manufofi bisa manyan tsare-tsare, tare kuma da zurfafa hadin kai irin na samun nasara tare, da cimma ra'ayi bai daya, don ciyar da tattalin arzikin duniya gaba yadda ya kamata.

Na biyu, shugabannin sun yi kuduri aniyar kirkiro sabbin hanyoyin neman ci gaba, don kara farfado da tattalin arzikin duniya. A yayin taron kolin, kungiyar G20 ta zartas da shirin neman ci gaba ta hanyar kirkiro da wasu matakai, da nufin mai da hankali kan kirkire-kirkire a fannin kimiyya, hakan zai taimaka wajen inganta kirkire-kirkire kan manufofin bunkasuwa, da tsarin cinikayya, kana da inganta cin gajiyar nasarorin da aka samu sakamakon kirkire-kirkire.

Na uku, shugabannin sun yi imani da kyautata tsarin sarrafa tattalin arziki da hada-hadar kudi na duniya don daga karfin tinkarar kalubalen tattalin arzikin duniya.

Na hudu, sun yi imani da farfado da muhimmiyar rawar cinikin kasa da kasa da zuba jari don bullo da tsarin tattalin arziki mai bude kofa ga duniya.

Na biyar, sun yi imani da sa kaimi ga samun ci gaba ta hanyar yin hadin gwiwa, don amfanawa dukkan duniya ta hanyar hadin gwiwar dake tsakanin membobin kungiyar G20.(Bilkisu/Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China