A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwararsa ta kasar Koriya ta kudu Madam Park Geun-hye a birnin Hangzhou.
Yayin ganawar tasu, Mista Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin na fatan zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Korea ta kudu a fannoni daban-daban bisa tsarin hadin kai tsakanin bangarorin daban-daban, da kuma kara yin mu'ammala kan wasu manyan batutuwan dake jawo hankalin kasa da kasa.
A nata bangare, Madam Park Geun-hye ta nuna cewa, shekarar badi ita ce shekarar cika shekaru 25 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, a don haka ya kamata Sin da Korea ta kudu su yi amfani da wannan zarafi mai kyau don zurfafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu.
Ban da wannan kuma, shugabannin kasashen biyu sun yi musayar ra'ayi kan halin da ake ciki a zirin Koriya. Mista Xi ya nuna cewa, Sin tana dukufa kan kawar da makaman nukiliya a zirin da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ya ce, ya kamata a warware wannan batu ta hanyar yin shawarwari. Kuma Sin tana matukar nuna rashin jin dadi kan matakin Amurka na girke na'urar kakkabe makamai masu linzami a Koriya ta kudu, a ganinsa rashin warware wannan batu cikin daidaito, zai iya kawo illa ga zaman lafiya a wannan yanki tare da kara haifar da sabani tsakanin bangarori masu ruwa da tsaki. Game da wannan batu, Madam Park Geun-hye tana fatan kara yin mu'ammala da kasar Sin. (Amina)