Hua Chunying ta shedawa 'yan jaridu cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi shi ne ya jagoranci taron ministoci tare da takwarorinsa na kasashe 10 da suka hada da na Rasha, Afrika ta kudu, Koriya ta kudu, Indonesiya, Mexico, da Singapore.
Wang ya fada a lokacin kaddamar da taron cewa, dukkanin kasashen duniya suna da alaka ta kut da kut da junansu sakamakon shirin nan na dunkulewar duniya wuri guda, kuma ya kamata duniya ta lura da muhimmancin gina dunkulalliyar al'umma ga dukkan jama'ar duniya, domin yin aiki tare don samar da sabuwar hanyar dangantaka da nufin samar da hadin kai don cin moriyar juna.
Hua, ta fada cewa, ministocin harkokin waje na kasashen, sun yi musayar ra'ayoyi game da wasu manyan batututwa da suka hada da: yaki da ta'addanci, 'yan gudun hijira, sauyin yanayin duniya, da samar da dawwamamman ci gaban duniya. (Ahmad Fagam)