A cikin jawabin da ya gabatar, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin kasuwanci a tsakanin Masar da Sin Mustafar Ibrahim, ya bayyana cewa, ganin yadda tattalin arzikin duniya ke cikin halin rashin tabbas, an kira wannan taro a daidai lokacin da ya dace. Yana kuma sa ran za a cimma cikakkiyar nasara a taron, da fatan kuma taron zai haifar da babban tasiri ga tattalin arzikin duniya.
Har wa yau, Amr Moussa, mashahurin masanin ilmin tattalin arziki na Masar, kana tsohon mataimakin babban bankin kasar yana ganin cewa, jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a gun taron kolin masana'antu da kasuwanci na G20 da ya gudana a ranar 3 ga wata, ya mika wani babban sako na hadin kan duniya domin samun ci gaba, hakan kuma ya samar da wani tsarin hadin gwiwa ga duniya, wajen gudanar da harkokin tattalin arziki.(Lubabatu)