Taron kolin na kwanaki biyu, wanda aka gudanar a ranakun Asabar zuwa Lahadi, gabannin fara taron koli na G20, ya samu halartar shugabannin kasuwanci sama da 1,100 daga kasashen duniya dabam dabam inda aka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi halin matsi da tattalin arzikin duniya ke fuskanta.
Taron kolin na B20 ya gabatar da rahoto game da shawarwari da aka bayar ga kungiyar G20, wanda ya kunshi muhimman shawarwari 20 da aka bayar, da kuma makatai da za'a dauka kimanin 76.
A karon farko rahoton ya gabatar da shawarwari, da suka hada da samar da yanayin kasuwancin na'urorin zamani a duniya, da dabarun kirkire kirkire da nufin bada kwarin gwiwa ga masana'antu, da kuma samar da kudaden zuba jari a fannin aikin gona.
Mahalarta taron sun hada da shugabannin kasashen Argentina, da Afrika ta Kudu, Australiya, Canada, da kuma shugabannin asusun bada lamuni na duniya IMF, dana bankin duniya WB, da sauran shugabannin kungiyoyi na kasa da kasa, inda suka tattauna da shugabannin kasuwanci.
A yayin taron sun amince cewa, mambobin G20 za su karfafa hadin kai ta hanyar bude kofa, da kuma samar da sauye sauye da bunkasa cigaba.(Ahmad Fagam)