in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sace kusan dalar Amurka dubu 530 a babban Bankin Somaliya
2016-08-26 10:51:11 cri
Gwamnan babban Bankin Somaliya, mista Bashir Issa ya shaida cewa kusan dalar Amurka dubu 530 ne aka sace a baban Bankin kasar. A cewar mista Issa, a halin yanzu ana tuhumar mista Muhidin Hassan wani ma'aikaci mai kula da ajiya a bankin da sace wadannan kudade, inda ya rika amfani da canjin dalar ta Amurka da kudin jabu. Ofishin 'yan sanda kasar da aka dorewa nauyin gudanar da bikince, na fadi tashin domin cafke wasu sauran mutanen da ake zargi da suka hada da wasu ma'aikatan baban Bankin. A shekarun baya ma, gwamnatin Somaliya ta fuskanci irin wannan matsalar ta satar kudin kasa. Kuma wannan lamarin ya faru a daidai lokacin da kasar take shirin shirya zabuka ba na kai tsaye ba da zasu gudana a cikin watannin Satumba da Oktoba.(Laouali Souleymane).
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China