in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan bindiga dadi sun kai hari a wani ginin cin abinci dake bakin ruwa a Mogadishu
2016-08-26 11:04:39 cri
A jiya Alhamis ne wandannsu 'yan Bindiga dadi suka kai hari a wani wajen cin abinci dake bakin ruwa a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya, bayan fashewar boma bomai da aka dasa a cikin mota, maharan sun cigaba da yin barin wuta kan wannan dakin cin abincin. Motar da aka dana wa boma bomai ta fashe a kusa da wani gidan shakatawa da kuma wajen cin abinci da ke bakin ruwan Banadir kan gabar ruwa Lido, a cewar wasu ganau. Ba a dai samu asarar rayuka ba har yanzu.

Wasu majiyoyin 'yan sanda sun rawaito cewa jami'an tsaro sun yi musanyar wuta tare da mayakan kungiyar Al-Shabab, da har yanzu suke cikin ginin otel din.

Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan hari, amma sai dai kungiyar Al-Shabab na kai hare haren ta'addanci jehi jehi a birnin Mogadishu a cikin yakin da take ga gwamnatin Somaliya. (Laouali Souleymane).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China