in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya tana neman mutane 3 ruwa a jallo bisa zarginsu da alaka da Boko Haram
2016-08-15 10:59:24 cri

A jiya Lahadi rundunar sojin Najeriya ta bayyana neman wani dan jarida guda da wasu mutane biyu ruwa a jallo, sakamakon zarginsu da alaka da kungiyar Boko Haram.

Dan jaridar da dakarun Najeriyar ke nema shi ne Ahmed Salkida, kasancewar shi ne mutumin da ya yi ikirarin cewar kungiyar Boko Haram ta tura masa faifan bidiyo dake nuna cewar kungiyar ta kashe wasu daga cikin 'yan matan sakandaren Chibok a daidai lokacin da dakarun Najeriyar ke kaddamar da hare hare ta jiragen sama.

Sauran mutanen biyu su ne, Jakada Ahmed U. Bolori da Aisha Wakil.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar kanal Sani Kukasheka Usman ya fadi hakan cikin wata sanarwa da ta iske kamfanin dilancin labaru na Xinhua cewa, ana neman mutanen 3 ruwa a jallo ne, domin bincikarsu game da alaka da mayakan na Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriyar ta zargi mutanen uku da laifin boye bayanai game da halin da 'yan mata Chibok ke ciki, da inda ake tsare da su a halin yanzu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China