An yi taron ganawa na kwarya-kwarya a tsakanin shugabannin kasashen kungiyar BRICS a yau Lahadi a birnin Hangzhou, shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Indiya Narendra Modi da shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma da shugaban kasar Brazil Michel Temer da kuma shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin sun halarci taron.
A gun taron, shugaba Xi ya yi jawabi, inda ya yi maraba da shigowar shugaban kasar Brazil Michel Temer cikin kungiyar BRICS. Ya kuma bayyana cewa, kasashen kungiyar BRICS suna da muhimmin matsayi a tsakanin kasashe masu tasowa, kuma su ne muhimman kasashe membobin kungiyar G20. Ya kamata kasashe membobi daban daban su kara yin hadin gwiwa da cimma daidaito domin kara taka rawa kan harkokin duniya.(Lami)