Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa sauyin yanayi na kawo illa ga rayuwar bil'adama da makomar duniya. Yarjejeniyar Paris ta shata hanyar dangantakar kasa da kasa kan yaki da sauyin yanayi domin bayan shekarar 2020, kana ta shaida wani shirin dake kan hanyar wani tsarin mulki na gari bisa dangantaka, da moriyar juna, bisa daidaici da adalci game da sauyin yanyi.
Ta hanyar mika dukkan wadannan takardu nasu, Sin da Amurka sun nuna burinsu da shiryyarsu na fuskantar kalubalen duniya, in ji Xi Jinping. (Maman Ada)