A yau Asabar da yamma, an bude taron kolin B20 a birnin Hangzhou, babban birnin kasar Zhejiang, taron da ya kasance na masana'antu da kasuwanci na kungiyar G20, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tare da gabatar da jawabi.
Taron B20 yana daya daga cikin muhimman harkokin da za a gudanar a yayin taron kolin G20 a birnin Hangzhou, wanda kuma ya kasance wani muhimmin dandali ga masu masana'antu da 'yan kasuwa na duniya wajen sa hannun gudanar da harkokin tattalin arziki da tsara ka'idojin ciniki a duniya. Wakilai sama da 800 na bangaren masana'antu da kasuwanci wadanda suka fito daga kasashe da shiyyoyi 32 da ma kungiyoyin duniya 26 sun halarci taron na wannan karo.(Lubabatu)