A yau Asabar 3 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU a wannan karo, kana shugaban kasar Chadi, Idriss Déby a birnin Hangzhou na Sin.
Shugaba Xi ya yi maraba da zuwan mista Idriss Déby don halartar taron kolin G20 da za a fara a birnin Hangzhou a madadin kungiyar AU, kuma ya nuna goyon baya ga kasashen Afirka da su ba da gudummawa wajen shiga aikin kulawa da harkokin duniya da sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin duniya.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, karfafa hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, manufa ce da Sin take bi cikin dogon lokaci. Sin za ta kokarta gudanar da shirin hadin gwiwa guda 10 bisa manufar da ta dauka kan kasashen Afirka, sa'an nan za ta hada bunkasuwar Sin da ta kasashen Afirka a gu daya, da nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen kara saurin bunkasa masana'antu da aikin gona na zamani, da zummar samun moriyar juna da samun ci gaba tare. Sin tana nuna goyon baya ga kungiyar AU da ta taka muhimmiyar rawa wajen raya kasashen Afirka da samun ci gaba tare da daidaita harkokin duniya da na shiyya shiyya baki daya.(Fatima)