A yayin ganawar, shugaba Xi ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su bunkasa dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata, kana da bin manufar magance rashin jituwa da kiyayya, tare kuma da girmama juna, da hadin kai don samun nasara tare.
Shugabannin biyu sun bayyana cewa, kasashen Sin da Amurka suna da moriyar bai daya kan harkokin Asiya da Pasific. Ya kamata bangarorin biyu su ci gaba da yin mu'ammala da hadin kai, da magance bambamce bambamce dake kasancewa a tsakaninsu yadda ya kamata. Bugu da kari, shugabannin biyu sun amince da karfafa hadin kai kan wasu muhimman batutuwan shiyya, da tinkarar kalubalen duniya, sun bayyana cewa, za su yi kokari tare da kasashen duniya, don warware wasu matsaloli yadda ya kamata, da kuma taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya, da samun wadata a duniya. (Bilkisu)