160904-laouali-souleymane-ana-sa-ran-ganin-kasar-sin-ta-taimakawa-farfadowar-tattalin-arzikin-duniya-Ahmad.m4a
|
Laouali Souleymane, wani kwararren dan jarida ne daga jamhuriyar Nijar, kuma ya halarci taron na kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya wato G20 dake gudana a birnin Hangzhou na kasar Sin, a matsayinsa na daya daga cikin mambobin tawagar 'yan jaridun kasashen duniya daban daban dake halartar kwas na horaswa a nan kasar Sin.
A yanzu haka kai tsaye muna tare da Laouali Souleymane, wanda ya samu halartar taron a birnin Hangzhou inda zamu ji irin abubuwan da ya ganewa idonsa a wajen.