in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in kai agaji na MDD zai ziyarci Sudan ta kudu
2016-07-31 12:33:42 cri
A mako mai zuwa wani muhimmin jami'in ofishin jin kai na MDD zai kai ziyarar kwanaki 3 a kasar Sudan ta kudu, domin duba halin jin kai da ake ciki a kasar da nufin kai dauki ga mutanen da suke cikin mawuyacin hali.

Bisa wata sanarwa daga ofishin jami'in hukumar bada agaji ciki gaggawa na MDD, an ce, Stephen O'Brien, mai ba da taimako ga babban sakataren MDD wanda ke kula da harkokin samar da kayayyakin jin kai cikin gaggawa a MDD zai kai ziyarar ne daga ranar 1 zuwa 3 ga watan Augusta.

Wannan sanarwa ta ce, a lokacin ziyararsa ta kwanaki uku a kasar Sudan ta kudu, Mr. Stephen O'Brien zai gana da mutanen da rikicin Sudan ta kudun ya shafa, da jami'an gwamnatin kasar, da kuma ma'aikatan ba da agaji na kasashen waje.

Dubban fararen hula ne rikicin baya bayan nan ya raba su da gidajensu a Juba da Wau, kuma suna fama da matsalar karancin abinci da yunwa a duk fadin kasar, da kuma barkewar cutar kwalara a Juba da kuma Jonglei. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China