Kungiyar IGAD ta yi alla wadai da kungiyar ta'addancin da take dauka mai hannu ga tashin bam guda biyu a ranar Lahadi a birnin Galkayo, dake arewacin Somaliya, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 20 da jikkata wasu 25.
Muna da imanin cewa wadannan munanan hare-hare ba za su karya hanzarin gwamnatin Somaliya da na al'ummar Somaliya ba wajen gudanar da zabuka, da suka kasance wani aikin siyasa mafi muhimmanci da tarihi da 'yan kasar baki daya suke tsimin jira, in ji sakatare janar na kungiyar IGAD, Mahboub Maalim, a cikin wata sanarwa a birnin Mogadiscio.
Mayakan Al-Shabaab sun dauki alhakin fashewar boma boman da aka dasa cikin wasu motoci biyu da ta shafi wani ginin gwamnatin wurin dake kusa da wata kasuwa dake cike da mutane.
Mista Maalim ya bayyana cewa kungiyar gabashin Afrikan za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin Somaliya bisa wani cikakken burin sake gina kasar da ya kasance babban fatan alheri na daukacin al'ummomin Somaliya da suke fama da matsaloli iri guda na duniya baki daya. (Maman Ada)