in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar FAO na neman tallafi domin gudanar da ayyukan agaji a arewa maso gabashin Najeriya
2016-08-10 10:59:09 cri

Hukumar samar da abinci da ayyukan noma ta MDD ko FAO a takaice, ta kaddamar da wani gangamin tallafawa kimanin mutane 385,000 a arewa maso gabashin Najeriya.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Talata, yana mai cewa FAO na bukatar kudi da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 10, domin samar da irin shuka, da takin zamani, tare da kayayyakin noman rani ga al'ummun da tashe-tashen hankula masu alaka da kungiyar Boko Haram suka shafa.

A cewar Mr. Haq, hukumar ta FAO ta lura da yadda sana'o'in noma da kamun kifi suka fuskanci gagarumin koma baya a 'yan shekarun nan, ko da yake a yanzu an samu wata babbar dama, ta tallafawa mazauna yankunan da a baya Boko Haram din ta yiwa kaka gida.

Har wa yau hukumar ta ce dawo da ayyukan noma a yankin arewa maso gabashin Najeriyar zai taka muhimmiyar rawa, wajen tabbatar da cewa al'ummun dake karbar 'yan gudun hijira a yankin, da ma wadanda suka kauracewa gidajen su, sun samu isasshen abinci yadda ya kamata.

Tashe-tashen hankula masu alaka da kungiyar Boko Haram dai sun hallaka mutane, wadanda yawan su ya kai 20,000, tare da raba wasu miliyan 2 da dubu dari biyu da muhallan su. Ko da yake yanzu haka dakarun hadin gwiwa dake yaki da dakarun kungiyar na samun galaba a yakin da suke yi da gyauron 'yan ta'addan.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China