Mista Mafa ya shedawa manema labarai a birnin Maiduguri, hedkwatar jihar Borno, cewa fiye da shanu dubu 169 da raguna da awaki dubu 63 aka rasa a lokacin wadannan hare hare daban daban.
Mista Mafa ya kara da cewa, masu gadin dabbobi sun kuma rasa gidajensu da aka kiyasta zuwa Naira biliyan 26, kimanin dalar Amurka miliyan 92 a cikin wadannan hare haren Boko Haram.
Shugaban ya kuma bayyana cewa, yankunan da suka fi fama da hare haren Boko Haram sun hada da Kala Balge, Mafa, Munguno, Bama, Konduga da Gwoza.
Najeriya ta samu cigaba a cikin yakin da take da Boko Haram a cikin shekara guda, rundunar sojojin Najeriya ta kwato yankunan kasar da dama da a lokacin baya suke hannun kungiyar Boko Haram. (Maman Ada)