in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan gudun hijirar Syria dake zaune a Girka zai shiga gasar Rio ta nakasassu
2016-08-31 13:50:29 cri
Dan gudun hijirar Syria mazaunin kasar Girka mai suna Ibrahim Al Hussein, na daya daga cikin wadanda za su shiga gasar Olympic ajin nakasassu ta birnin Rio, wadda za ta gudana cikin watan Satumba mai zuwa.

Al Hussain shi da wani dan gudun hijirar mai suna Shahrad Nasajpour daga Iran mazaunin kasar Amurka, za su zamo mambobin tawaga mai zaman kan ta, kamar dai yadda kwamitin Hellenic mai kula da bangaren 'yan wasan ya bayyana.

Tuni dai shugaban wannan kwamiti Yorgos Fountoulakis, ya tabbatar da hakan, yana mai cewa sun yi farin cikin ganin 'yan gudun hijirar biyu sun cimma burin su na zama daya daga wadanda za su halarci wannan gasa mai matukar tarihi.

Wannan ne dai karon farko da 'yan gudun hijira za su shiga gasar ta nakasassu, bayan da wata tawagar makamanciyar ta, ta shiga gasar da aka kammala ta ajin masu cikakkiyar lafiya a 'yan kwanakin baya.

An dai fara sanin Al Hussein ne yayin da ya wakilci 'yan gudun hijira wajen daga wutar Olympic a cikin filin wasa na birnin Athens, gabanin mita wutar ga kasar Brazil wadda ke karbar bakuncin gasar Olympic din ta bana.

Ana dai sa ran Al Hussain zai shiga gasar linkaya ajin maza ta mita 50 da mita 100, bisa jagorancin kocin sa dan kasar Girka Eleni Kokkinou.

Al Hussein dai ya rasa wani bangare na kafar sa ne, yayin tashin wani Bam a shekarar 2012. Ya kuma yi jinya a wani asibiti dake kasar Turkiyya, kafin ya ketara teku zuwa kasar Girka inda yake samun mafaka.

Da yake bayyana farin cikin sa dame da wannan batu, Al Hussain ya ce shiga gasar Olympic ya kasance wani mafarki ne na sa tun kusan shekaru 22 da suka gabata. Ya ce yayi tsammanin ba zai samu wannan dama ba har abada bayan da ya rasa kafar sa. Amma yanzu yana cike da farin ciki ganin wannan dama ta samu. Ya ce sakon sa ga daukacin wadanda suka jikkata sakamakon yake yake shi ne, ko wannen su na iya cika burin sa na rayuwa.

Halartar sa wannan gasa tare da Nasajpour zai zamo wata hanyar gabatar da sakon miliyoyin 'yan gudun hijira da masu neman mafaka, dama yada dabi'ar gasar Olympic ta nakasassu, wato karfafa gwiwar al'umma da kuma nuna juriya.

'Yan gudun hijirar su biyu za su bayyana a yayin bikin bude gasar a ranar 7 ga watan Satumba. Za kuma su kasance tare da sauran 'yan wasa su kimanin 4,350, a tsangayar 'yan wasa da aka tanada, inda 'yan wasa daga kasashe da yankuna 165 za su sauka.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China