160728-Kudurin-da-IOC-ta-yanke-game-yan-wasan-Rasha-ya-haifar-da-mahawara-a-New-Zealand-zainab.m4a
|
Wannan batu dai ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin sassan biyu, duba da a hannu daya, yadda (NZOC) ta fidda sanarwar amincewa da matakin na IOC, yayin da a daya hannun kuma DFSNZ wadda a baya ke goyon bayan dakatar da daukacin 'yan wasan Rashan daga shiga wannan gasa, ke ganin sabon matakin na IOC, tamkar tarnaki ne ga 'yan wasan Rashan, wadanda ke kiyaye dokar da ta jibanci mu'amala da miyagun kwayoyi.
Ita dai IOC ta dauki wannan mataki ne na yiwa 'yan wasan Rasha tantancewar kwaf, bayan da aka gabatar da rahoton "McLaren", wanda ya tabbatar da zargin da ake yi wa wasu daga hukumomin Rashan da hannu, wajen daukar nauyin 'yan wasa masu mu'amala da miyagun kwayoyi, ko kuma basu kariya.
Yanzu dai IOCn za ta bukaci 'yan wasan na Rasha, masu shirin shiga gasar birnin Rio da su gabatar da cikakkiyar shaidar nuna biyayya ga ka'idojin gasar, da kuma bada dama ta a yi musu gwaji a wajen kasar su.(Saminu Alhassan)