Kamfanin dillancin labarai na Agencia Brasil ne ya rawaito Mr. Dubi na bayyana hakan a ranar Asabar. Jami'in ya ce ko da a watanni biyu da suka gabata ma, sai da aka gabatar masa da cikakken tsari na tsaron da aka tanada, wanda kuma bayan harin da ya auku a kudancin kasar Faransa aka kara inganta yanayin sa.
Dubi ya ce batun ta'addanci batu ne da ba za a iya raba wani yanki na duniya da shi ba, don haka abun da yake wajibi shi ne daukar matakai na dakile shi a dukkanin sassa na duniya.
A wani ci gaban kuma 'yan sanda a Mato Grosso do Sul na kasar ta Brazil, sun tsare mutum na 11 da ake zargi da shirya kaddamar da wani hari, yayin gudanar gasar ta Olympic dake tafe. Wanda ake zagin dai ya mika kan sa ne ga 'yan sanda, bayan da aka ayyana sunayen mutane 12, cikin jerin wadanda aka samu bayanan sirri game da manufar su. Yanzu haka dai mutanen na can tsare gidan yarin birnin Mato Grosso dake kasar ta Brazil.(Saminu Alhassan)