Jami'an kafafen yada labarum kasar Brazil, wato Agencia Brasil sun bayyana cewa, daliban zasu samu kyautar kudaden zirga zirga, dana wuraren kwana, dana abinci rana, da kuma rigunan wasannin motsa jiki na nakasassu.
Za'a baiwa yaran da suke da nakasa fifiko wajen rabon tikitin.
Agencia Brasil ya ce; " manufar aiwatar da wannan shiri shine, domin baiwa kananan yara damar sanin al'amurran wasanni, da wasannin nakasassu"
A cikin wannan watan, kwamitin shirya wasannin Olympic, da gwamnatin kasar Brazil sun raba tikiti kimanin 55,000 ga yara 'yan makaranta a wasannin kwallon kafa, dana badminton, dana kwallon tebur, da wasannin dambe da dai dauransu.
Za'a gudanar da wasannin nakasassune tsakanin ranakun 7 zuwa 18 ga watan Satumba.(Ahmad Fagam)