Kafafen yada labarun kasar sun rawaito cewa, La Cruz ya isa El Retiro makwabciyar kasar ne, daga tsakiyar birnin Camaguey, bayan shafe tsakiyar dare yana tafiya a wata mota kirar jeep, yayin da dandazon mutane ke zaune a gaban gidansa suna jiran isowarsa.
Dan dambe mai shekaru 27 da haihuwa yace; "nayi matukar farin ciki da irin wannan karba da aka shirya mini, da kuma irin goyon bayan da alummar Cuba suka nuna mini har ta kaini ga nasarar lashe lambar zinare".
Game da gasar damben Olympic kuwa, dan wasan yace, "wannan shine wasan da nafi samun cigaba cikin wasannin damben dana shafe sama da shekaru 20 ina yi".
Ya bayyana cewar ya dauki wannan wasan ne tamkar wani abin sha'awa, bayan wata shawara da tsohon dan wasan kwallon raga Yumilka Ruiz ya taba bashi.
La Cruz, wanda ya samu nasara har sau 3 a wasannin duniya, yayi nasarar lashe lambar zinare a wasannin Rio, kuma wannan shine cikon dukkanin lambobin yabon da kungiyar wasan dambe ta duniya AIBA ta tsara.(Ahmad Fagam)