Jami'ar dai ta yi wannan yabo ne kwana guda bayan ta ki amincewa da karbar masaukin da aka basu, wanda tace akwai 'yan matsaloli da suka shafi bandakunan, da toshewar wasu bututan ruwa.
Sai dai a cewar Kitty Chiller, an samu gagarumin cigaba, kuma ta jaddada cewar akwai yiwuwar tawagar 'yan wasan zasu sauka a masaukin a ranar Laraba kamar yadda suka tsara tun da farko.
A cewar Chiller, ya zuwa ranar Lahadi akwai matsaloli sama da 200 da suka shafi wuraren kwanan bakin. Sai dai Australia ta kashe kudaden don tsabtace masaukin a aljihunta, kuma har yanzu, ba'a sanar da ita ba ko za'a dawo mata da kudaden data kashe ko a'a.
Magajin garin Rio Eduardo Paes, yana ta kokarin kwantarwa da tawagar 'yan wasan na Australiya hankali, ta hanyar shirya wanda zasu yi musu tarba ta musamman zuwa masauklin.
Chiller ta yabawa Paes, da kuma kananan kwamitocin tsare tsare bisa irin kokarin da suka nuna wajen shawo kan matsalar.
Tawagar 'yan wasan daga kasashen Birtaniya, da Argentina, da New Zealand, da Brazil da kuma Italy suna fama da matsaloli da suka shafi masaukin da aka tanadar musu.