in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude masaukin wasannin Rio Olympic a hukumance
2016-07-27 14:57:20 cri
A ranar Lahadi ne aka kaddamar da katafaren ginin masaukin mahalarta wasannin Rio Olympic, kawo yanzu an kammala shirye wuraren zama kusan 3,600 domin saukar jami'an da zasu halarci wasannin daga dukkan sassan duniya baki daya.

Shahararren dan wasan kwallon kwandon nan mai shekaru 47 Janeth Arcain, wanda shine magajin garin da za'a gudanar da wasannin, ya jagoranci bude masaukin mahalarta wasannin tare da magajin garin Rio de Janeiro Eduardo Paes, da kuma shugaban kwamitin shirya wasannin Carlos Nuzman, dukkansu sun jagoranci bude filin wasan a hukumance.

Katafaren ginin wanda ke dauke da gidaje 31 da kuma dakunan kwana 3,604, inda za'a sauke 'yan wasan sama da 7,000 da jami'an kungiyoyin 'yan wasan sama da 6,000 har tsawon lokacin kammala wasannin Paralympic.

Wasu daga kungiyoyin 'yan wasa na kasashen waje tuni har sun fara sauka a wajen, kuma ya kunshi wuraren motsa jiki na sa'oi 24, da wuraren ajiya, da banki, da wuraren aika sakonni, da wuraren gyaran gashi, da wuraren dafa abinci wanda zai iya samar da abinci dubu 60 a kowace rana har tsawon lokacin kammala wasannin.

Sai dai a cewar mai Magana da yawun masu shirya wasannin na Rio 2016, Mario Andrada, har yanzu babu wasu kungiyoyin wasanni na Rasha da suka isa wajen.

Tun da farko kwamitin shirya wasannin na Olymphic wato IOC ya yanke shawarar cewa bazai sanyawa Rasha takunkumin shiga gasar ta Rio Olympics ba, sai dai ya mika batun ga hannun hukumar shirya wasannin bazara ta kasa da kasa (IF) a matsayin wacce zata yanke hukunci game da cancantar mahalarta wasannin.

Nuzman ya fada bayan bikin bude masaukin mahalarta wasannin cewar, wannan shawarace data shafi IOC da IF.

Za'a fara wasannin na Olympics ne daga ranar 5 zuwa 21 ga watan Augusta, sannan a gudanar da wasannin Paralympics tsakanin 7 zuwa 18 ga watan Satumba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China