Wani jami'i ya bayyana cewa, ma'ajiyar makamai da hadarin ya faru yana birnin Garaboll mai nisan kilomita 60 daga gabashin birnin Tripoli. Kafin fashewarta din, sojojin dake kula da ma'ajiyar sun yi rikici tare da fararen hula dake wurin, amma daga baya sojojin sun janye daga wannan wurin. Fararen hula dake wurin sun yi kangiya kan hanyar motoci a tsakanin Garaboll da Misrata.
Wannan jami'i ya kara da cewa, ana bincike kan dalilin fashewar bom din, an riga an kai mutane da suka ji rauni zuwa asibiti, kuma akwai yiyuwar yawan mutanen da suka mutu zai karu. (Zainab)