in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta horas da dakarun wanzar da zaman lafiya domin samar da tsaro a zaben Somaliya dake tafe
2016-08-14 13:04:19 cri

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika AU dake Somaliya wato (AMISOM), ta horos da dakarunta domin su taimaka wajen samar da tsaro a lokacin zaben kasar Somaliya dake tafe.

A wata sanarwa da aka fitar a jiya Asabar, mataimakin kwamishinan 'yan sandan AMISOM Christine Alalo, ya bukaci 'yan sandan kasar Ugandan dake aiki a rundunar kiyaye zaman lafiyar dake kasar Somaliya da su taimakawa jami'an tsaron kasar a lokacin zabukan kasar da za'a gudanar a watannin Satumba da Oktoba na wannan shekara.

Alalo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin kammala bada horo ga jami'an 'yan sandan 100 na FPU wadanda ke aikin karkashin AMISOM.

Tawagar jami'an 'yan sandan ta FPU za su taimakawa 'yan sanda Somaliya da kuma bada kariya ga dakarun AMISOM, da na MDD da sauran jami'an tarayyar Afrika dake kasar Somaliya.

Alalo ya bukaci dakarun na Ugandan da su yi aiki tare da 'yan sandan Somaliya da sauran jami'an tsaro na sauran kasashen duniya, domin tabbatar da zaman lafiya a kasar Somaliya wadda ke fama da hare haren kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Al-Shabaab.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China