Jakadan kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya ce kasashe masu wakilci a kwamitin tsaron MDD, za su ci gaba da bada gudummawa wajen tattauna hanyoyin gudanar da sauye-sauye ga tsarin ayyukan kwamitin na tsaro.
Mr. Liu ya ce aikin gyaran fuska ga tsare-tsaren kwamitin na tsaro, nauyi ne dake wuyan mambobin kwamitin, gwargwadon matsaya da kuma tunanin su. Ya ce yayin babban taron majalissar, mambobin ta sun yi zuzzurfar mahawara game da manyan batutuwa 5, wadanda suka jibanci ayyukan kwamitin tsaron majalissar MDDr.
Sin ta yi maraba da kwazon jagorantar babban zaman majalissar Mogens Lykketoft, da jakadan Luxembourg a MDD Sylvie Lucas, wanda ke shugabancin ayyukan kwamitin na gyaran fuska tun cikin watan Oktobar bara. Mr. Liu ya ce Sin na fatan za a dora inda aka tsaya game da wannan muhimmin aiki yayin babban taron MDDr dake tafe, a hannu guda kuma dukkanin sassan masu ruwa da tsaki za su ci gaba da tattaunawa, domin cimma nasarar da aka sanya gaba.
Tuni dai babban zaman MDDr ya amince da sanya aikin gyaran fuska ga kwamitin tsaron MDD cikin ayyukan taron majalissar na gaba.(Saminu Alhassan)