Bayan tattaunawa ta tsawon lokaci wanda kasashen Amurka da Rasha suka jagoranta, kungiyoyin kasa da kasa dake fafutukar tabbatar da zaman lafiya a Syria, sun amince da'a shigar da kayayyakin tallafi zuwa kasar.
Da yake jawabi ga manema labaru a yau Jumma'a, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce, shirin tsagaita wutar a fadin kasar na tsawon mako guda, zai ba da damar shigar da kayayyakin jin kai ga dinbin fafaren hula dake cikin mawuyacin halin a kasar.
Ya kara da cewar, kawo yanzu ba'a bayyana yadda shirin tsagaita wutar zai gudana ba.
Sai dai mahalarta taron tattauna kan batun tsagaita wutar sun bukaci da a maido da batun tattaunawar zaman lafiya ta Geneva. (Ahmad Fagam)