Lou Jiwei wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi, ya ce jami'an kudi da na manyan bankunan kasashe mambobin kungiyar G20, sun yanke shawara kan wasu muhimman fannoni guda 9 da wasu manufofi da za su kasance jagora ga yin gyare-gyare guda 48, matakin da ministan ya ce wani babban ci gaba ne da aka samu. Ya ce jami'an sun kuma lashi takwabin karfafawa manyan bankunan raya kasa gwiwar kara zuba jari a bangaren samar da muhimman kayayyakin more rayuwa ta yadda za a kara hade duniya waje guda.
Bugu da kari, jami'an sun amince su dora muhimmanci kan raya kanana da matsakaitan masana'antu, yin takara tsakanin kudade da nuna adawa da karya dokokin cinikayya.
Wannan shi ne karon farko da masu tsara manufofi suka amince su yi amfani da harkokin kudi, matakan yin gyare-gyare domin samar da daidaito da kara samun bunkasuwa. Sun kuma amince a gudanar da gyare-gyare a bankin duniya da asusun ba da lamuni na duniya.
Ana sa ran gabatar da sakamakon abubuwan da aka tattauna a yayin taron kolin G20 da zai gudana a birnin Hangzhou da ke nan kasar Sin. (Ibrahim Yaya)