Cibiyar nazarin tattalin arziki ta Bruegel dake birnin Brussels ta bayar da bayani a kwanakin baya inda ta yi nuni da cewa, Sin na kara ba da tasirinta a duniya, kuma kasar tana kara taka muhimmiyar rawa a tsarin gudanar da hada-hadar kudi na duniya.
A ganin masanan na kasashen Turai, bayan faruwar rikicin hada-hadar kudi na duniya a shekarar 2008, kungiyar G20 ta zama muhimmin bangare wajen sa kaimi ga gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da hada-hadar kudi a duniya. A karkashin kokarin kasar Sin a bana, kungiyar G20 ta fara yin kwaskwarima kan tsarin gudanar da hada-hadar kudi na duniya, ciki har da batun maida hankali kan tsarin tsaron harkokin hada hadar kudi, da amfani da ikon samun kudi na musamman na asusun bada lamani na IMF bisa la'akari da ma'aunin tattalin arziki na SDR, da yin kwaskwarima kan tsarin hada-hadar kudi na duniya da dai sauransu, wadanda za su kawo babban tasiri ga tsarin gudanar da hada-hadar kudi a duniya. (Zainab)