Ministan harkokin wajen kasar Liberiya Marjon Kamara ya bayyana cewa, gwamnatin kasarsa ta nuna goyon baya kan matsayin da Sin ta dauka kan wannan batun, a ganinta, ya kamata a warware batun ta hanyar yin shawarwari bisa dokokin kasa da kasa da abin ya shafa.
A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Senegal Mankeur Ndiaye ya bayyana cewa, kafin wannan hukunci, Sin da Philippines sun taba cimma daidaito kan warware batun tekun kudancin Sin ta hanyar yin shawarwari, dangane da haka, kasar Senegal ta yi kira ga kasashen da abin ya shafa da su bi daidaiton da aka cimma, da warware batun ta hanyar yin shawarwari, da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a tekun.
Ban da wannan kuma, mataimakin shugaban kwamitin kungiyar AU Erastus Mwencha ya bayyanawa 'yan jarida cewa, bisa ra'ayin AU, hanya mafi kyau wajen warware batun tekun kudancin Sin ita ce yin shawarwari na kai tsaye tsakanin bangarorin da abin ya shafa. (Zainab)