A kwanakin baya, babbar jami'ar kasar Australia ta yi furuci game da hukuncin da aka yanke kan batun tekun kudancin kasar Sin cewa, hukuncin yana da karfi, ya kamata bangarori daban daban su bi hukuncin, kana kasar Australia tana da ikon ratsa da keta sararin sama bisa tanadin dokokin kasa da kasa.
Game da wannan batu, Lu Kang ya bayyana cewa, Sin ta riga ta tuntubi kasar Australia, domin bayyana mata rashin amincewarta.
Lu Kang ya kara da cewa, hukuncin da aka yanke ba zai yi tasiri ga ikon mallakar tekun kudancin kasar Sin da moriyar tekun, kuma kasar Sin ta nuna rashin amincewarta ga duk wani irin aikin da za a gudanar bisa hukuncin. (Zainab)