Scholz memba na kungiyar GUE / NGL ta majalisar dokokin Turai da ya zo daga kasar Jamus. A wannan rana, ya bayyana a cikin wani sakon E-mail da ya turawa manema labaru, ya nuna cewa, hukuncin da kotun yanke hukunci ta Hague ta yanke ba zai maye gurbin shawarwarin da kasa da kasa suka yi don warware batun tekun kudancin kasar Sin ba. Ya ce, tilas ne kasashen da abin ya shafa su fara yin shawarwari cikin hanzari, wadanda ya kamata su maida hankali ga fannoni uku wato magance yin yaki, tabbatar da tsaron zirga-zirga, da kuma yin hadin gwiwar moriyar juna.
Scholz ya jaddada cewa, ana bukatar bangarori daban daban da abin ya shafa su girmama da amincewa da juna, wanda zai taimakawa wajen warware wannan matsala. Sin ta riga ta bayyana ra'ayinta na fatan yin shawarwari, ya kamata kasashen dake yankin su bi sahun kasar Sin. (Zainab)