Mista Adesina ya bayyana wa 'yan jarida a kwanan nan a birnin Nairobi cewa tattalin arzikin kasashen Afrika zai samu wani adadin bunkasuwa da kashi 4.7 cikin 100 a shekarar 2017. Kasashen gabashin Afrika suke a sahun gaba kuma sun samu cigaban mai kyau da ya kai kashi 6 zuwa 7 cikin 100 a wadannan shekarun baya bayan nan, in ji jami'in.
Wannan tsohon ministan Najeriya ya tabo misalin Kenya, Tanzaniya, Rwanda, Mozambique, RDC-Congo da kuma Cote d'Ivoire a matsayin kasashen da suka samu cigaba mai armashi ta fuskar bunkasuwa.
Amma kuma mista Adesina ya yi gargadi bisa ganin cewa Afrika na fuskantar kalubaloli kamar faduwar farashin man fetur ko kuma bambance-bambancen kasafin kudi tsakanin kasashen Afrika. (Maman Ada)