Babbar daraktar bankin na EADB Vivienne Yeda, ta fada cewar, aikin gano ma'adinan da hako su zai yi matukar sanya al'ummomin yankunan dake da arzikin sa zulumin cin moriya, sannan gwamnatocin kasashen zasu samu damar cike gibin kasafin kudinsu da zarar aka samu nasarar hako ma'adinan, kana rayuwar al'ummomin yankunan zata inganta.
Yeda ta fada a lokacin taron bita wanda EADB ya shiryawa alkalan kasashen gabashin Afrika a birnin Nairobi cewar, abu mafi muhimmanci shine kasashen dake da arziki ma'adinai su fi amfana daga aikin hako su.
Ta kara da cewa, ya zama tilas alummomin dake zaune a yankunan masu arzikin su amfana musamman wajen samar su da ayyukan yi, da bada damar kasuwanci, da biyan haraji, da basu kwarewa da horo domin cin gajiyar ayyukan yadda ya kamata.
Yeda tace, domin samun nasarar cimma wannan burin, kamata yayi hukumomin tattara haraji, dana kiyayae muhalli, dana walwalar jama'a su maida hankali wajen tsara hanyoyin da zasu tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin kasashen nasu.
Da yake jawabi a yayin rufe taron bitar, ministan shari'a na kasar Kenya, Githu Muigai, ya bukaci lauyoyin gwamnati na kasashen, dasu tabbatar da cewa arzikin ma'adinai dake kasashen an sarrafa su ta yadda za su samar da hanyoyin habaka cigaban tattalin arzikin kasashen.
Muigai yace, daukar wadannan matakai zai tabbatar da samun guraben ayyukan yi ga jama'a, sannan zai takaita gurbatar muhalli idan har aka aiwatar da tsare tsare yadda ya kamata.(Ahmad Fagam)