Babban jami'in bankin duniya mai lura da nahiyar Afirka Makhtar Diop, ya ce bankin zai yi hadin gwiwa da kasashen nahiyar Afirka, wajen baiwa kasashen damar cin gajiyar sabon salon tattalin arziki mai dogaro da albarkatun nahiyar, a matsayin wani mataki na fidda al'ummun kasashen daga kangin talauci.
Mr. Diop, wanda ya bayyana hakan ga mahalarta wani taron karawa juna sani a birnin Nairobin kasar Kenya, ya ce wannan sabon salo na bunkasa tattalin arziki na iya bada damar samar da abinci mai gina jiki, da karin guraben ayyuka, da wadata, tare da fadada kafofin inganta tattalin arzikin nahiyar.
Ya ce sassan da wannan manufa ta shafa sun hada da zuba jari a bangaren gudanar da mulki mai nagarta, da gina ababen more rayuwar jama'a, tare da samar da kyakkyawan muhalli ga masu zuba jari a fannoni masu zaman kansu.
Jami'in ya ce duk da matsalar sauyin yanayi dake dakushe ribar da ake samu daga albarkatun ruwa, kamata ya yi masu ruwa da tsaki su bada gudummawa wajen ganin an ci gaba da cin gajiyar wannan fanni.
Kaza lika Mr. Diop, ya ja hankalin shuwagabannin Afirka da su tabbatar da aiwatar da kudurorin ci gaba mai dorewa na MDD, domin cimma nasarar kare albarkatun ruwa, musamman duba da alkaluman dake nuna cewa yawan al'ummun Afirkan dake amfana daga wannan sashe sun kai mutum miliyan 12.(Saminu Alhassan)