Kamfanin samar da hidima na kasa da kasa mai suna Ernst & Young wanda ya bayyana hakan a yau Litinin, ya kuma bayyana cewa, an samu karuwar jarin da aka zuba kai tsaye daga ketare a shekarar 2015, inda ayyukan jarin da aka zuba ya karu da kashi 7 cikin 100 .Kamar yadda kamfanin na EY ya bayyana cikin rahotonsa dangane da shirye-shirye wadanda suke janyo hankulan masu sha'awar zuba jari a nahiyar Afirka wanda ya fitar a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, koda ya ke jarin ayyukan ya kan yi kasa a kowace shekara, daga dala biliyan 88.5 a shekarar 2014 zuwa dala biliyan 71.3 a shekarar 2015. Har yanzu wannan adadi ya dara na matsakaicin adadi na shekarar 2010 zuwa 2014, kimanin dala biliyan 68.(Ibrahim)