Tun daga shekarar bara, salon bunkasa tattalin arzikin kasar Sin ya ragu, amma kusan dukkan masana'antun da suke bunkasa sabbin sana'o'in zamani sun samu ci gaba sosai. Sakamakon haka, sun zama muhimman ginshikai wajen tabbatar da samun ci gaban tattalin arziki da kyautata tsarin sana'o'in da kuma neman kirkiro wasu sabbin sana'o'in zamani. Alkaluman kididdiga na nuna cewa, yawan ribar da wadannan masana'antu 27 wadanda suke bunkasa sabbin sana'o'in zamani ke samu ya karu da kashi 15.9 cikin kashi dari a tsakanin watan Janairu zuwa Mayu na bana. (Sanusi Chen)