in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika uku za su shiga hukumar ATI
2016-07-07 10:36:19 cri
Hukumar bunkasa kasuwanci da inshora ta Afrika ATI ta tabbatar da cewar kasashen Zimbabwe, da Habasha, da Kwadifwa za su shiga hukumar nan da karshen watan Satumba.

Babban jami'in ATI George Otieno, ya sanar da hakan a yayin zantawa da manema labarai a Nairobi babban birnin kasar Kenya, ya ce tuni shirye shirye sun yi nisa na shigar kasashen Zimbabwe da Habasha da Kwadifwa.

Otieno ya ce, suna fata majalisun kasashen za su tabbatar da amincewar kasashen nasu su shiga ATI nan da watanni 2 zuwa 3 masu zuwa.

Ana sa ran kasashen uku za su rattaba hannu kan yarjejeniyar hukumar ta ATI, ta yadda za su baiwa hukumar kariya daga duk wata barazanar siyasa da za'a iya fuskanta daga kasashen nasu.

Ita dai hukumar ATI ta kasance hadin gwiwa ce ta kasuwanci da zuba jari na kasashen Afrika, wadda a yanzu haka kasashen Afrika 10 ne suke rike da ragamarta, da suka hada da kasashen Malawi, da Dimokaradiyar Congo, da Zambia, da Uganda, da Rwanda, da Tanzania, da Burundi, da Benin da kuma Madagascar.

An kafa ATI a shekarar 2001, kuma ta fara ne da kasashen Afrika 7, manufar kafata shi ne samar da tsarin Inshora ga kasashen, wanda shi ne babban kalubalen dake haifar da matsalar gudanar da al'amurran kudi a kasashen.

Otieno ya ce dukkanin mambobi kasashen za su iya samun kudaden rance mai karancin kudin ruwa daga babbar cibiyar samar da kudade ta ATI. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China