in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zimbabwe ya sanar da gyara manufar sauya kamfannoni masu jarin waje zuwa na gida
2016-04-13 14:44:31 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Gabriel Mugabe ya ba da sanarwa a kwanan baya, inda ya gyara manufar sauya kamfanoni masu jarin waje zuwa na gida, hakan ya kwantar da hankulan 'yan kasuwa.

Majalisar dokoki ta kasar Zimbabwe ta gabatar da dokar sauya kamfanoni masu jarin waje zuwa na gida da kuma ba da ikon gudanar da harkokin tattalin arziki a shekarar 2007, wadda ta kayyade cewa, dole 'yan asalin kasar Zimbabwe su rike yawancin hannun jari na kamfanoni masu jari sama da dala dubu 500, wadanda kuma kasashen waje suka zuba jarin ko kuma fararen fata na kasar suka kafa.

Amma wannan doka ta samu adawa sosai bayan da aka gabatar da ita. A kwanan baya, hukumomin da abin ya shafa na kasar Zimbabwe sun kalubalanci kamfannoni masu jarin waje da su mika takardar shirin sauyawa zuwa kamfannoni masu jarin gida kafin ranar 31 ga watan Maris, lamarin ya haifar da tashe-tashen hankali a kasuwannin kasar Zimbabwe sosai.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China