in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mugabe ya yi bikin murnar cika shekaru 92 a duniya
2016-02-23 10:41:01 cri
A ranar Litinin da ta gabata jami'ai dake aiki a ofishin shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe sun gudanar da bikin taya murnar cika shekaru 92 da haihuwar shugaban kasar wanda ya samu matsayi na kasancewa shugaban kasa mafi tsufa a duniya.

Bisa al'adar bikin, ma'aikatan sun gabatar da kyautukan taya murna domin nuna farin cikinsu.

Mugabe, wanda mai dakinsa Grace ta rufa masa baya tare da dansa da kuma 'yarsa, da sauran makusanta daga danginsa a yayin bikin, wanda aka gudanar a fadar gwamnati, bikin ya samu halartar mataimakin shugaban kasar Phelekezela Mphoko da ministoci da dama.

An haifi Mista Mugabe a watan Fabrairun shekarar 1924, kuma shi ne jagoran gwagwarmayar kwatan 'yancin kasar daga 'yan mulkin mallaka a shekarar 1980, kuma tun daga wancan lokaci ne yake ci gaba da jan ragamar mulkin kasar.

Bisa ga dokokin kundin tsarin mulkin kasar, an amince da Mugabi ya sake neman wa'adin mulki a zaben shugabancin kasar da za'a gudanar a shekarar 2018, kuma zai iya ci gaba da jan akalar kasar har zuwa shekarar 2023 a lokacin da shekarunsa na haihuwa za su kai 99. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China