in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD tana maraba da jadawalin zaben kasar Somaliya
2016-08-10 10:36:09 cri

Sakataren janar na MDD Ban Ki-moon ya sanar a jiya Talata cewa, ya gamsu da jadawalin shirye-shiryen zaben shugaban kasar Somaliya wanda ake sa ran gudanarwa a karshen watan Oktoban wannan shekara.

A ranar Lahadi ne hukumar zaben kasar Somaliya ta fitar da jadawalin zaben kasar, inda ta bayyana cewar za'a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar daga ranar 24 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Oktoba, sannan za'a gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 30 ga watan Oktoba.

Jami'an gudanarwar kasar Somaliya ne suka amince da wannan mataki, a yayin wani taron da suka gudanar a ranar Talata game da shirye-shiryen zaben kasar yake tafe.

A sanarwar da mai magana da yawun sakatare janar na MDD ya fitar, Ban ya ce, zaben kasar Somaliya na 2016 wata alama ce dake nuna aniyar kasar ta komawa turbar demokaradiyya, sannan ya bukaci dukkannin bangarorin kasar da su kaucewa duk wani mataki da zai haifar da jinkiri game da shirye-shiryen zaben kasar.

Ban, ya yabawa kokarin hukumar zaben kasar musamman sabo da ware kashi 1 bisa 3 na kujerun majalisar dokokin kasar ga 'yan takarkari mata, inda ya bayyana cewar, hakan wata alama ce dake nuna samun cigaban gwamnatin siyasa a kasar.

Kasar Somali ta tsunduma cikin rikici ne tun a shekarar 1990, tun bayan kifar da gwamnatin sojin karkashin shugabancin Siad Barre. Kuma tun daga wancan lokacin ba'a gudanar da zabe a kasar ba.

A halin yanzu kasar na fuskantar barazanar kungiya Al-shabab mai tsattsauran ra'ayi, wacce ta sha kaddamar da hare hare domin kifar da gwamnatin kasar ta Somaliya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China